An cafke matar al-Baghdadi a Lebanon | Labarai | DW | 02.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke matar al-Baghdadi a Lebanon

Wata majiyar soji a Lebanon ta ce rundunar sojojin ƙasar ta kama matar jagoran Ƙungiyar masu jihadi ta IS Abu Bakr al-Baghdadi a kusa da kan iyaka da Siriya.

Majiyar ta ce ana tsare da matar da kuma ɗanta a wata cibiyar hukumar leƙen asiri ta soja da ke a garin Yarze kusa da Beyrouth tun kwanaki goman da suka wuce.

Matar wacce 'yar asilin ƙasar Siriya ce an kamata da ɗanta mai kimanin shekaru takwas zuwa tara a kusan daga garin Arsal tare da fasfo na jabu. A cikin wata Yunin da ya gabata ne al Baghdadin Ƙungiyarsa ta IS ta yi iƙirarin kafa daula a cikin ɗaukacin ƙasashe musulmi.Yanzu haka dai ƙungiyar na kai mummunar hare-hare a Iraƙi da Siriya.