An cafke kakakin tsohon shugaban Libiya
October 20, 2012
Tsohon kakakin fadar shugaban Libiya Muhamar Gaddafi, na yanzu haka tsare a cibiyar tsaro ta ƙasar Libiya bayan da aka cafke shi a wani shingen binciken ababen hawa a wannan Asabar. Tun a shekarar bara ne lokacin ana tsananin zanga-zanga a ƙasar Libiya,Moussa Ibrahim kakakin hambararen shugaban ya yi batan dabo a kasar bayan da aka bada sammacin kamun sa. Ana zarginsa ne da bada umurnin hallaka ɗaruruwan 'yan tawaye a wancan lokacin.
Wannan kamun ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar Libiya ke tuni da zagayowar mutuwar hamɓararren shugaban wanda kuma wasu ƙungiyoyin kare hakin bil adama suka nuna bukatar gudanar da binciken mutuwarsa ciki har da Amnesty International da ta kira Majalissar Ɗinkin Duniya da ta maida hankali a kan batun.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar