An bukaci hukunta jami′an CIA | Labarai | DW | 11.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci hukunta jami'an CIA

Bayan fidda rahoton azabtar da fursunoni wanda jami'an tsaron Amirka suka yi, an nemi gabatar wadanda suka bada umarinin yin hakan.

An ci-gaba da samun kiraye-kirayen ganin sai an gabatar da man'yan jami'an gwamnatin Amirka a kotu, bisa bada umarni wa hukumar leken asiri ta CIA izinin ganawa fursunoni azaba. MDD ta ce dole jami'an da suka shirya lamarinsu fiskanci shari'a, bisa take yancin dan Adam. Shugaban kasar Afganistan Asraf Ghani, yace almarin na CIA ya sabawa dukkan wani nau'i na yancin dan Adam fadin duniyar nannan. Ghani yace lamarin da matukar zafi, rahoton na majalisar dattawan Amirka ya nuna yadda aka azabtar da wasu daga fursunaoni da basu ma san komai kan ta'addanci.