1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci a tuhumi Benjamin Netanyahu

Ahmed Salisu
December 2, 2018

'Yan sanda a Isra'ila sun bukaci a tuhumi firaministan kasar Benjamin Netanyahu kan zargin cin hanci da wasu karin laifuka da ake yi masa tare da mai dankinsa Sara.

https://p.dw.com/p/39Hva
Israelischer Premier Benjamin Netanjahu
Hoto: picture alliance/NurPhoto/C. Marquardt

Jami'an 'yan sandan suka ce binciken da suka gudanar ya nuna cewar akwai hujja kwakkwara da za a iya amfani da ita wajen gurfanar da shugaban gaban kuliya, sai dai Netanyahun da mai dakin nasa sun musanta yin ba daidai ba inda firaministan ya ce an tado da maganar ce don a yi masa illa a siyasance.

Tuni da 'yan jam'iyyun adawa musamman shugaban jam'iyyar Labour Avi Gabbay suka bukaci firaministan na Isra'ila da ya yi murabus. Wannan dai shi karo na uku a 'yan watannin nan da aka bukaci tilastawa firaministan fuskantar shari'a kan zargin aikata ba daidai ba.