1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

GMF:Taron 'yan jarida na kasa da kasa

Abdoulaye Mamane Amadou
June 20, 2022

A karon farko tun bayan bullar annobar corona, a gaba da gaba an bude taron 'yan jaridun duniya da kafar yada labarai ta DW ke shiryawa shekara-shekara.

https://p.dw.com/p/4Cx9i
Plenary Session: Who’s got the power in the media landscape? Part 1
Hoto: DW/F. Görner

Taron da zai shafe tsawon kwanaki biyu a na gudanar da shi a birnin Bonn, zai mayar da hankali kan kalubalen da 'yan jarida suke fuskanta a yayin da yake-yake ke kara ta'azara a duniya, kana da ma duba barazanar canjin yanayi, baya ga wasu tarin matsalolin da 'yan jarida ke fuskanta a ko ina cikin duniya.

Batun yakin Ukraine da Rasha na a wasu daga cikin muhimman batutuwan taron, duba da yadda ya janyo gibi da tangarda ga tattalin arikin duniya.

Wannan ne farko shekaru da dama bayan bullar annobar corona, da ake taron da ke zama karo na 15 gaba da gaba, ana kuma shirin  karrama wasu 'yan Ukraine biyu da lambar yabo saboda gudummawar da suka bayar ta musamman don sanar da duniya game da gaskiyar haklin da ake ciki a yakin da Rasha ke gwabzawa da Ukraine.