1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude sabon babi a Zimbabuwe

Ramatu Garba Baba
November 24, 2017

Ermmerson Mnangagwa ya yi rantsuwar kama aiki a wani lamari da ke nuni da rufe shafi na mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe wanda ya shafe shekaru 37 a kan karagar mulki tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai.

https://p.dw.com/p/2oCN4
Simbabwe Harare Vereidigung Präsident Emmerson Mnangagwa
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Dan shekaru 75 da haihuwa Mnangagwa ya yi rantsuwar kama aiki a filin kwallo cike makil da jama'a da ke a wajen birnin Harare, hakan kuma na zuwa ne kwanaki uku bayan da shugaba Robert Mugabe mai shekaru 93 da haihuwa ya yi murabus a sakamakon matsin lamba daga 'yan kasar da ma jam'iyyarsa ta ZANU-PF. A filin kwallon na wajen birnin Harare sabon shugaban ya yi jawabi inda ya jinjina wa al'ummar kasar ta Zimbabuwe.

Simbabwe Harare Vereidigung Präsident Emmerson Mnangagwa
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Tun da sanyin safiya al'ummar birnin Harare, suka yi cincirindo a filin kwallon kafa domin ganewa idanunsu shagulgulan wannan rana mai babban mahimmanci a gare su. Duk da cewa al'ummar a birnin Harare da ta halarci biki na cike da farin ciki, a hannu daya kuma abun da ke cikin zukatansu, shi ne irin kamun ludayin sabon shugaban kasar.

A daren 14 zuwa 15 ga wannan wata na Nuwamba ne sojojin kasar ta Zimbabuwe suka yi wani hobbasa tare da kwace iko daga hannun shugaba Mugabe, amma kuma suka ce ba wai juyin mulki ba ne illa kawai matakin kakkabe 'yan ta'adda da ke kewaye da shugaban, wadanda su ne suka hana ruwa gudu a cikin tafiyar kasar. Hakan ya faru ne bayan da shugaba Mugabe ya kori mataimakin nasa da suka yi mulkin kasar tare tun daga shekara ta 1980, amma kuma uwargidan tsohon shugaban Grace Mugabe ta sa aka kore shi sabili da yadda ta ke kallon shi a matsayin wani babban cikas wajen cika burinta na cin gadon maigidanta na shugabancin kasar ta Zimbabuwe.