An bankaɗo taɓargazar cin hanci a Faransa | Labarai | DW | 03.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bankaɗo taɓargazar cin hanci a Faransa

Tsohon ministan kasafin kuɗin ƙasa mai marabus Jerome Cahuzac, ya tabbatar da cewar ya mallaki miliyan dubu ɗari shidda a cikin Bankunan a ɓoye.

Gwamnatin Faransa na shirin gabatar da wani ƙudirin doka a gaban majalisar dokoki, na bayyana ƙadarori da dukiya da manyan jami'an gwamnati da yan majalisu suka mallaka.

Hakan kuwa ya biyo bayan da wani tsohon ministan na kasafin kuɗi na ƙasar Jerome Cahuzac ya tabbatar da cewar ya na da kuɗaɗen ajiye a cikin bankuna kusan shekaru 20 da suka wuce. Shugaba Francois Hollande wanda shi ne ya bayyana ɗaukar matakin, ya yi Allah wadai da abin da ya kira abin takaici da kuma cin amanar ƙasa. Ya ce :'' Kuskure ne da ba za a taɓa yafe wa ba,kasance wa da kuɗaɗen ajiya a cikin Bankuna a ƙasashen waje ba tare da sanar da hukumomi ba.''

Tun can da farko dai ministan wanda ya yi marabus a cikin watan jiya, ya ƙayarta zargin kafin daga baya akan matsin lamba na yan sanda ,ya sanar da cewar ya mallaki kuɗaɗen.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman