1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sallamo tsohon Firaministan kasar Malesiya

Zulaiha Abubakar MNA
September 20, 2018

Tun da fari an zargi tsohon Firaministan da laifin cin hanci da rashawa kafin daga baya a kuma bankado wasu laifuffuka har 25 da suka hada da amfani da mukaminsa wajen cin amanar kasar.

https://p.dw.com/p/35GOW
Malaysia Kuala Lumpur Najib Razak vor Gericht
Hoto: Reuters/L. S. Sin

An sallamo tsohon Firamistan kasar Malesiya Najib Razak bayan da hukumar yaki da yiwa dukiyar kasar ta'annati  tsare a ranar Laraba sakamakon wasu kudade da aka same shi da su ajiye a banki.

Tun da fari an zargi tsohon Firaministan da laifin cin hanci da rashawa kafin daga baya a kuma bankado wasu laifuffuka har 25 da suka hada da amfani da mukamin sa wajen cin amanar kasar, kodayake ya karyata wadannan zarge-zarge.

Babbar kotun kasar dai ta bayar da belinsa kan kudi Dala dubu dari 845.