1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da tura dakarun Majalisar Dinkin Duniya Mali

Mohammad AwalFebruary 6, 2013

Kasashen yammacin Afirka da na yammacin duniya sun amince da tura dakarun Majalisar Dinkin Duniya Mali don yin aikin wanzar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/17Ymj
Hoto: dapd

Kasashen dai sun ce sun amince da daukar wannan matsayi domin dakarun na Majalisar Dinkin Duniya su maye gurbin dakarun da kasashen Afrika su ka yi karo-karo wanda yanzu haka dakarun Franasa ke jagoranta a gumurzun da ake na fatattakar masu kaifin kishin addini daga wasu sassa na arewacin Mali din da su ka karbe iko da shi a watannin baya.

Masu sanya idanu kan halin da ake ciki a kasar ta Mali dai na ganin cewar amincewar da taron ya yi game da wannan batu ba zai rasa nasaba da kokakrin da dakarun Faransa da na sauran kasashen Afrika su ka yi cikin kankanin lokaci ba na fattatakar 'yan tawayen daga yankunan da su ke.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan batu, mukaddashin sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da harkokin siyasa Jeffery Feltman cewa ya yi wannan matsayi da su ka dauka ba wai kasar Mali kadai zai taimakawa ba, har ma da yankin Sahel baki daya.

Mali Konflikt
Dakarun kasashen AfrikaHoto: AFP/Getty Images

''Ya ce warware mawuyacin halin da yankin Sahel ke ciki zai taimaka mana kuma zai taimaki al'ummar Mali. Idan mu ka taimaka aka warware matsalolin da Mali ke fuskanta wanan ko shakka babubu zai taimaka wajen wasu daga cikin matsalolin da yankin Sahel ke fuskanta''

Shi ma dai shugaban hukumar kungiyar kasashen Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO Kadre Ouedraogo na da irin wannan tunani domin kuwa a cewarsa wannan matsala fa ba a Mali ta tsaya ba.

''Ya ce matsalar da yanzu haka ake fuskanta a Mali ba wai matsala ce da za ta faru ta kare a cikin kasar ba, kazalika ba matsala ce da za ta shafin yammacin Afrika ba ko ma nahiyar baki daya ba, matsala ce ta tsaro da ta shafi duk duniya''

Krise im Norden von Mali
Masu kaifin kishin addiniHoto: Reuters

Yayin da Mr. Felt da Mr. Ouedraogo ke wadannan kalamai biyo bayan amincewar da taron ya yi na aikewa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya don wanzar da zaman lafiya a Mali din, ministan harkokin wajen kasar Tieman Coulibaly cewa ya yi gwamnatinsu ta yi nadamar halin da kasar ta tsinci kanta a ciki inda ya ce dama abinda ya dace shi ne kasashen duniya su hada karfi da karfe wajen korar masu kaifin kishinn addini.

''Ya ce ba da son ran mu ne aka shiga wannan yaki ba, tilas ta mana aka yi. Yakin ya jawo mana asara mai dunbin yawa. Mun yi nadamar fararen hular da yakin ya shafa da ma wanda 'yan tawaye su ka muzgunawa a baya. Mu na ba mutane da abin ya shafa hakuri. Dole ne kasashen duniya da mu baki daya mu hadu wajen ganin mun fatattaki wadannan mutane masu kaifin kishin addini daga kasar mu''

To yayin da ake daura da cimma wannan daidaito, a hannu guda kuma kasar Faransa ta bakin ministan harkokin wajenta ta sanar da cewar za ta janye dakarunta da ke kasar cikin watan gobe idan Allah ya kaimu duba da abinda ta kira cigaba da aka samu bayan da ta karbe yankunan da 'yan tawaye su ka mamaye, yayin da a hannu guda kuma shugabannin kasashe ke ta kai gwaro su na kai mari da nufin ganin nan da watanni shidda an maida kasar kan tafarkin demokradiyya duk kuwa da cewar masu fashin bakin siyasa na ganin abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.

Krise im Norden von Mali Flüchtlinge
'Yan gudun hijirar MaliHoto: Reuters

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal