An ƙara tsaurara matakan tsaro a Masar | Labarai | DW | 02.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ƙara tsaurara matakan tsaro a Masar

An baza jami'an tsaro a kusa da fadar shugaban ƙasar a jajibirin taho mu gama ɗin da a ka yi a harabar wanda a cikin wani mutumin ya rasa ransa

Ƙungiyar yan addawa ta yi kira ga minista tsaro da ya yi marabus bayan wani hoton bideyo da aka nuna wanda ke nuna jami'an tsaron na dukar wani mutumin da ke a tsirara a gaban fadar shugaban ƙasar.

Sannan wasu rahotannin na cewar masu yin zanga zangar a dandali Tahrir sun riƙa jefa butala akan hirar ministn ƙasar Hicham Qandil.Majiyoyin gwamnati sun ce mutane 53 suka rasa rayukan su a cikin tashin hankalin da ya bazu a cikin sauran garuruwan ya yin da wasu majiyoyin yan addawar ke cewar addadin waɗanda suka mutun ya kai 91.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman