Amurka zata maido da huldar kasuwanci da Vietnam | Labarai | DW | 09.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka zata maido da huldar kasuwanci da Vietnam

A wani labarin kuma majalisar ta wakilan Amirka mai rinjayen jam´iyar republicans ta kada kuri´ar amincewa da maido da huldar cinikaiya da kasar Vietnam. To sai dai ba´a sani ba ko wani zama na musamman da majalisar dattijai zata yi a karshen wannan mako zai amince da wannan shiri domin har yanzu wasu ´yan majalisar na nuna adawa da ba da wannan garabasa ta cinikaiya wadda Vietnam da Haiti da yankin Andrean da kuma wasu kasashe masu tasowa su kimanin 100 zasu ci gajiyar ta.