Amurka tayi alkawarin kara taimakawa Habasha | Labarai | DW | 21.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka tayi alkawarin kara taimakawa Habasha

Kasar Amurka ta sanarda bada taimakon fiye da dala miliyan 25 na jin kai ga kasar Habasha da take fama da tsananin karancin abinci.

Mataimakin shugaban hukumar raya kasashe ta Amurka USAID,Micheal Hess,yace wannan taimako ya hada da taimakon abinci na dala miliyan 17 da kuma dala miliyan 8 da dubu dari uku don taimakawa mata da yara kanana.

Hess a karshen rangadinsa zuwa yankin gabashin Afrika inda miliyoyin mutane suke fuskantar yunwa,yace wannan kudi kari ne bisa wanda Amurka ta alkawarta tun farko na dala miliyan 48.

Ya fadawa manema labarai a birnin Addis Ababa,cewa, ya gamsu da yadda ake gudanar da aiyukan samarda abinci a yankin,yace,mafi yawan kudin zai tafi ne ga allummomin makiyaya da balain fari yafi rutsawa sa su.