Amurka: Sakamakon binciken harin Kunduz | Labarai | DW | 25.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka: Sakamakon binciken harin Kunduz

Hukumar binciken da Amurka ta nada ta gano cewar, harin da aka kai kan asibitin Kunduz da ke arewacin Afganistan kuskure ne a bangaren sojojin Amurka.

Hafsan sojin Amurka da ke jagorantar rundunar kasar da ke Afganistan ya ce harion ranar 3 ga watan Oktoba akan wani asibiti da ke karkashin kulawar kungiyar likitoci ta kasa da kasa da ke kunduz kuskure ne aka samu. Janar John Campbell ya na bayani ne kan sakamakon harin sojin Amurkan da ya yi sanadiyyar kashe mutane 30 tare da raunata wasu 37.

A birnin Kabul fadar kasar gwamnatin Afganistan ne ya gabatar da wannan rahoto na hukuma mai zaman kanta daga ketare, mai shafuka 3,000.

Campbell ya ce " sojojin Amurka da ke da hannu a wannan hadarin basu san cewar wannan ginin asibi ne da ke karkashin kulawar kungiyar likitocin kasa da kasa ba. Sun kai harin ne bisa zaton cewar wani gini ne mai nisan daruruwan mitoci daga inda asibitin yake, inda aka ce musu akwai mayakan sakai. Kazalika jami'an da suka bayar da umurnin kai harin da wadanda suka zartar da shi, ba su yi la'akari da tabbatar da cewar ginin ne, kafin su kai harin ba".

Daura da kuskure a bangaren sojojin a cewar hafsan rundunar Amurkan, an kuma samu matsala ta lalacewar na'urar sadarwa da ke cikin jirgin. Campbell ya ce babu kasar da ta kai Amurka kare hakkin fararen hula, amma a wannan karon an samu kuskure.