1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a binne George Floyd kusa da mahaifiyarsa

Ramatu Garba Baba
June 9, 2020

A wannan Talatar za a binne George Floyd da mutuwarsa ta haifar da zanga-zangar nuna adawa da zalunci da cin zarafin mutane masu launi da jami'an tsaron Amirka ke cigaba da yi.

https://p.dw.com/p/3dU66
USA Houston | Hunderte nahmen Abschied von George Floyd
Hoto: imago images/ZUMA Press/G. Vasquez

A Amurka, a yau Talata za a yi jana'izar George Floyd, mutumin da mutuwarsa ta janyo zanga-zanga a cikin Amurka da wasu sassan kasashen duniya. Za a binne dan shekara arba'in da shidan ne a kusa da mahaifiyarsa a wata makabartar da ke birnin Houston inda marigayin ya girma. A daya bangaren kotu ta nemi dan sandan da yayi ajalinsa da ya biya kudin beli na dala miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin.

A yayin da Amurkan ke shirin gudanar da babban zaben kasar a watan Nuwamban bana, batun kisan Floyd ya sami gurbi a batutuwan yakin neman zaben, kan goyon bayan masu zanga-zangar yin tir da cin zalin da 'yan sanda suke yi wa bakakken fata a kasar, tsohon mataimakin Shugaban kasa Joe Biden a karkashin inuwar jam'iyyar Demokrat, ne zai fafata da Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican a zaben shugaban kasar.