1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amsoshin Takardunku kan hali na kwarai

Ramatu Garba Baba MAB
January 16, 2023

Shirin ya amsa tambaya kan ko ana gadon hali daga iyaye musanman halayen da ba na kwarai ba? Wannan ya biyo bayan matakin da wasu ke dauka na zubar da cikin da aka samu ta hanyar fyade.

https://p.dw.com/p/4MGt6
Uwa da danta a Abujan NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Masana kimiyya sun sha shawartar jama'a da su kula da kyau domin kada su kamu da wasu nau'ukan ciwo da a kan iya gadonsu daga iyaye, kamar ciwon daji ko ciwon suga ya zuwa hawan jini da binciken na masana ya tabbatar ana iya gadonsu. Amma ya lamarin ya ke ta fannin hallaya? Dakta Bala Gadanga, likita a asibitin koyarwa na Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoton Najeriya ya yi cikakken bayani a game da gurbin gadon hallaya a kimiyance