Amsar Hollande ga kirar François Bozize | Labarai | DW | 27.12.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amsar Hollande ga kirar François Bozize

Kasar Faransa ta ki mara wa shugaban Bozize na Jamhuriyar Afirka ta tsakiya baya a yunkurin da ya ke yi na murkushe 'yan tawaye da suka kusa da Bangui babban birni.

Kasar Faransa ta sa kafa ta yi fatali da kirar da gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta yi mata, na mara mata baya domin ganin bayan 'yan tawayen da ke neman hambarar da shugaba François Bozize. A lokacin da ya ke tsokaci game da wannan batu shugaba Francois Holland na Faransa ya ce gwamnatinsa ba za ta yi shishshigi a harkokin cikin gida na wata kasa mai cin gashin kanta ba. Sai dai ya ce zai yi amfani da sojojinsa domin kare rayukan faransawa da ke rayuwa a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma ofishin jakadancin Faransa da aka kai wa hari.

'Yan tawayen da ake yi wa lakabi da seleka na ci gaba da nausawa Bangui babban birni, inda rahotannin suka nunar da cewa sun sake nasarar karbe ikon gari guda daga hannun dakarun gwamnati. A halin da ake ciki rundunar hadin guywa na kasashen yankin tsakiyar Afirka ta bayyana cewa za ta aika da dakarunta domin kare Bangi babban birni. Sai dai tuni Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka fara kwashe ma'aikatansu da zamansu bai zama bai wajabta ba a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita. Halima Balaraba Abbas

 • Kwanan wata 27.12.2012
 • Muhimman kalmomi RCA
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/179aL
 • Kwanan wata 27.12.2012
 • Muhimman kalmomi RCA
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/179aL