Amon harbe-harbe a birnin Bouake | Labarai | DW | 15.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amon harbe-harbe a birnin Bouake

Rahotanni daga Ivory Coast na cewa an jiwo amon harbe-harben bindiga a manyan birane biyu na kasar yayin da a waje guda rundunar sojin ta ce ta kaddamar da yunkurin maido da doka da oda.

Sojoji a Ivory Coast sun durfafi birni na biyu mafi girma a kasar a wani mataki da babban hafsan sojin kasar ya ce sun kaddama na kawo karshen boren da wasu sojojin suka yi na tsawon kwanaki uku game da biyan su wasu kudaden su na garabasa.

Akalla mutane biyar aka bada rahoton sun rasu sakamakon harbin bindiga a birnin Bouake lokacin da sojojin suka kaddamar da bore. Al'umma a kasar na cigaba da gangamin nuna adawa da boren sojin.

Jama'a a biranen Abidjan da kuma Bouake sun ce sun ji amon harbe-harben bindiga da safiyar yau Litinin abin da ke nuna cewa har yanzu kurar ba ta lafa ba.