1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Bama sun aikata cin zarafin dan Adam

Gazali Abdou Tasawa
June 27, 2018

Kungiyar Amnesty International ta zargi wasu shugabannin sojojin kasar Bama 12 da aikata laifin cin zarafin dan Adam kan tsirarrun Musulmi 'yan kabilar Rohingyas a jihar rakhine a 2017.

https://p.dw.com/p/30MZ9
Rohingya-Flüchtlinge in Bangladesch
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Dar Yasin

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Amnesty International ta zargi wasu shugabannin sojojin kasar Bama 12 da suka ba da umurnin farmakin da sojojin kasar suka kaddamar kan tsirarrun Musulmi 'yan kabilar Rohingyas a jihar rakhine da aikata laifin cin zarafin bil adama. 

Kungiyar ta bayyana wannan matsayi nata ne a wani taron manema labarai da ta shirya a wannan laraba inda ta sanar da aniyarta ta shigar da kara a gaban kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ta ICC. Tirana Hassan jami'ar kula da rigingimu a kungiyar ta Amnesty ta ce binciken da suka gudanar sun gano cewa sojojin kasar Bamar sun aikata fyade da kisan kai da azabatarwa, kone-kone da rushe-rushe da dai sauran ayyukan assha, wadanda laifuka ne masu girma da ya kamata a shigar da kara kansu a gaban kotun hukunta manyan lafukan yaki ta duniy ata ICC.

Daga watan Agusta zuwa na Disemban 2017 Musulmi 'yan kabilar Rohingyas sama da dubu 700 suka tsere daga kasar ta Miyammar zuwa makobciyarta ta Bengladeshe a sakamakon farmakin da sojojin kasar suka kai masu  a cikin jihar Rakhine inda suka hallaka mutane da dama da suka hada da kananan yara da mata.