Amnesty ta zargi Malta da Italiya | Labarai | DW | 01.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty ta zargi Malta da Italiya

Ƙungiyar Amnesty International ta ce ƙasashen Italiya da Malta sun gaza wajen kai agaji cikin gaggawa domin ceto rayukan baƙin haure.

Ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Amnesty International ta ce rashin kai agajin gaggawa a kan jirgin ruwa maƙare da baƙin haure da ya nutse a gabar tekun Malta a shekarar da ta gabata ta 2013,Shi ne ya haddasa mutuwar bakinn hauren masu yawa. Ƙungiyar ta ce da ƙasashen Italiya da Malta sun kai agaji cikin gaggawa da an ceto rayukan mutanen da suka mutu da kuma waɗanda suka ɓace a tekun. A watan Oktobar shekarar da ta gabata ne dai wani jirgin ruwa ɗauke da aƙallah baƙin haure 400 ya nutse a gabar tekun Malta inda sojojin ruwa na ƙasashen Malta da Italiya suka samu nasarar ceto wasu daga cikinsu, yayin da har kawo yanzu ba a samu nasarar gano sauran mutanen da suka ɓace a tekun ba.