Amnesty ta yi suka kan kare hakkin ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 10.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amnesty ta yi suka kan kare hakkin 'yan gudun hijira

A yayin da duniya ke bikin ranar kare hakkin dan Adam, reshen Jamus na Amnesty International ya ce maimakon amfani da kalmar "yan gudun hijira", kamata ya yi a ce wadanda ke neman tsira daga take hakkin dan Adam.

Saurari sauti 03:50

Rahoto kan suka da Amnesty ta yi kan kare hakkin 'yan gudun hijira

A yayin wani taron manima labarai da ta gudanar a Berlin na Jamus,Selmin Caliskan ta ce bata cika son kwatanta wadanda suka tsere daga kasashensu zuwa wasu wurare domin neman tsira daga take hakkinsu, a matsayin yan gudun hijira ba. Caliskan,wadda ita ce babbar sakatariyar reshen Jamus na kungiyar Amnesty International ta ce muna kyamar wannan kalma, saboda imanin da muka yi cewar tashe-tashen hankula a kasashensu ne suka tilasta wa wadannan mutane kaurace wa wuraren zamansu na asali. Tilas ne kuwa a dakatar da wadannan matakai na keta hakkin 'yan Adam, wadanda su ne suke zama sanadiyyar kaurar jama'a. Lokacin hira da manema labarai albarkacin wannan rana ta kare hakkin 'yan Adam, Caliskan ta ce wajibi ne a nuna wa wadanan mutane zumunci na hakika.

Amnesty International Bericht zu Usbekistan PK in Berlin Selmin Caliskan

Selin Caliskan ta Amnesty ta gudanar da taron manaima labarai a Berlin

Ta ce " Jamus na iyakacin kokarinta, saboda ta karbi mutane masu yawa, kuma ta na daya daga cikin kasashe 'yan kalilan da suka karbi mutanen fiye da kima. Amma a daya hannun, muna sukan kokarin da Jamus ke yi na bin sahun sauran kasasahen Turai da suka toshe iyakokinsu domin hana shigowar karin mutanen da suka kauracewa yankunansu".

Babbar sakatariyar ta kungiyar Amnesty ta yi nuni da dokar baya-bayan nan da ta kara tsananta manufofin karbar 'yan gudun hijira da zamansu a Jamus, ta kuma yi suka ga yarjejeniyar da ta shafi maida 'yan gudun hijirar kasashen da suka fito, muddin wadannan kasashe su na iya karbarsu, inda musamman ta yi suka ga yarjejeniyar da aka cimma da kasashen Masar da Iritiriya da Sudan.

Ta ce "Wadannan kasashe ne da su kansu suke take hakkin 'yan Adam, kuma suke da alhakin haddasa dalilan da ke sanya al'ummarsu tserewa zuwa ketare. Irin wannan yarjejeniya, mummunan illa ce ga 'yan gudun hijiran. Misali game da kasar Iritiriya. 'Yan Iritiriya na uku a rukunin 'yan gudun hijira da suka fi yawa d ake zuwa nan ta cikin teku".

Griechenland Flüchtlinge aus Eritrea vor Rhodos

'Yan Iritiriya na bin tekun don gudun cin zarafi daga hukumomin kasarsu

Kungiyar Amnesty International ta maida hankali ,musamman ga halin da ake ciki a kasashen da ke kewaye da Siriya, kasar da ke fama da yakin basasa a yanzu. Wadannan kasashe, inji kungiyar mai zaman kanta, su na bukatar agaji cikin gaggawa, domin baiwa mutanen da suka tsere daga Siriya din damar ci gaba da rayuwa cikiin walwala.

Amnesty ta yi kira da a dauki matakan sake tsugunar da akalla kashi 10% na 'yan gudun hijirar ya zuwa karshen wannan shekara ta 2015, musmaman mata da yara da marasa lafiya da wadanda suka yi fama da azabtarwa a kasarsu ta asali.

Sauti da bidiyo akan labarin