Amnesty ta ce ana ci gaba da keta hakkin dan Adam a duniya | Labarai | DW | 24.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty ta ce ana ci gaba da keta hakkin dan Adam a duniya

A rahotonta na bana kungiyar Amnesty International ta yi suka kan tabarbarewar 'yancin dan Adam a duniya baki daya.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce halin da 'yancin dan Adam ke ciki ya yi muni a duniya baki daya. A lokacin da take gabatar da rahoton shekara shekara na kungiyar a birnin Berlin, babbar sakatariyar Amnesty a Jamus Selmin Caliskan ta ce a cikin kasashe 122 daga cikin 160 da suka gudanar da bincike a cikinsu, sun gano cewa ana azabtarwa ko cin zarafin dan Adam. Kungiyar ta zargi gamaiyar kasa da kasa da rashin yin wani katabus don magance rikice-rikice a duniya. Lura da yawan 'yan gudun hijira miliyan 60 a duniya, kungiyar ta yi kira da a samar da sahihan manufofin kare hakkin dan Adam.