1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta bukaci rufe sansanin Guantanamo

Abdullahi Tanko Bala
January 8, 2022

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International ta bukaci shugaban Amirka Joe Biden ya rufe sansanin gwale gwale na Guantanamo da ke Cuba wanda a wannan watan ya cika shekaru 20 ana tsare mutane a cikinsa.

https://p.dw.com/p/45IU6
Protest gegen Folter
Hoto: Tim Sloan/AFP/Getty Images

Amnesty ta ce sansanin wata alama ce ta nuna izza da zalunci da kuma azabtarwa a cewar wani kwararren jami'in kare hakkin bil Adama dake Amirka Sumit Bhattachariyya.

Bhattachariyya ya kuma bukaci shugaba Biden ya hukunta dukkan wadanda ke da hannu wajen azabtar da jama'a a sansanin

A yanzu sansanin na da mutane 39 da suka rage ake tsare da su bisa umarnin tsohon shugaban Amirka George W Bush na tsare muslim da ake zargi da ta'addanci ba tare da shari'a bayan harin 11 ga watan Satumba 2001 da harin ta'addanci a New York da kuma Washington DC.

Shugaba Barrack Obama na jam'iyyar Democrat wanda ya gaje shi ya yi kokarin rufe sansanin amma abin ya ci tura saboda adawar da majalisar dokokin Amirka ta nuna yayin da a waje guda kuma Donald Trump na Republican ya nuna muradin cigaba barin sansanin a bude.

Amnesty ta kudiri aniyar gudanar da zanga zangar nuna alhini bayan shekaru 20 da kafa sansanin gwale gwalen na Guantanamo.