Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da sakaci | Labarai | DW | 09.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da sakaci

Ƙungiyar ta kare hakkin bil adama ta ce tun da farko sai da aka sanar da rundunar sojojin ƙasar cewar wasu 'yan bindiga za su kai hari a garin Chibok amma kuma ba su mayar da martani ba.

Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce tun da farko an gargaɗi rundunar sojojin Najerya da cewar 'yan ƙungiyar Boko Haram za su kai a hari a garin Chibok amma kuma ba su yi wani yunƙuri ba.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta bayyana ta ce shaidun da ta tattara sun nuna cewar sojojin rundunar sojin Najeriya ba ta ɗauki labarin da mahimmanci ba, cewar za a kai hare-hare a makarantar ta garin Chibok. Kuma ta ce sojoji ƙalilan kimanin 17 da ke a garin Chibok sun fice daga garin dangane da yadda 'Yan Ƙungizar Boko Haram suka fi ƙarfinsu

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu