1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilin nada Agnes Callamard shugabar Amnesty International

March 29, 2021

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta sanar da cewa daga wannan Litinin Agnes Callamard za ta fara aiki a matsayin sabuwar shugabar kungiyar ta duniya.

https://p.dw.com/p/3rJhw
Sonderberichterstatterin UN Agnès Callamard
Hoto: Elif Ozturk/AA/picture alliance

Sunan jami'ar ya fara fitowa ne bayan binciken kisan dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi da ta jagoranta a karkashin MDD. Kazalika ta kuma jagoranci bincike a kan kisan da Amurka ta yi wa  Janar Qasem Soleimani na Iran.

Ana fatar Agnes Callamard 'yar kasar Faransa za ta jagoranci Amnesty International a matsayin Sakatare-Janar na tsawon shekaru hudu. Abokan aikin jami'ar na mata fatar za ta jagoranci kungiyar  cikin nasara musamman ganin yadda ta ke da gogewa da masaniyar abubuwan da ke faruwa a kasashen duniya.

Amnesty International da aka kafa a shekarar 1961 a Burtaniya dai na da ofisoshi a kasashe fiye da 70 na duniya, kuma kungiyar na yi wa kanta lakabi da cewa ita ce babbar kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya.