1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ethopia : Amnesty da HRW sun soki yadda ake kisan jama'a

Abdoulaye Mamane Amadou
December 16, 2021

Kungiyoyin kare hakin bani Adama na kasa da Human Rights Watch da Amnesty international sun zargi mayakan sa kai masu kawance da dakarun gwamnatin Ethopia da laifin kisan fararen hula 'yan Tigrey.

https://p.dw.com/p/44NLM
Äthiopien | Verwüstungen in Lalibela
Hoto: AFP via Getty Images

A cikin wani rahoton hadin gwiwar da suka fitar, kungiyoyin biyu sun ce a cikin watannin Nuwanba da Disamba mayakan sa kai sun hallaka dimbin fararen hula ciki har da kananan yara da tsoffi a yammacin Tigrey.

Wannan rahoton na zuwa a yayin da hukumar kare hakin bil'Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gudanr da taron koli na musamman kan batun cin zarafin bani Adama a yankin Tigrey, tare da duba yiwuwar kafa wani kamitin bincike na musammam a kai.

Akalla mutane miliyan biyu ne suka kauracewa gidajensu don tsira da rai tun bayan da rikici ya barke tsakanin gwamnatin tsakiya da mayakn 'yan awaren Tigrey na Habasha baya ga wasu masu dumbin yawa da suka rigamu gidan gaskiya.