Amnesty: 2014 shekarar tarzoma a duniya | Labarai | DW | 25.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty: 2014 shekarar tarzoma a duniya

A rahotanta na shekara-shekara Kungiyar Amnesty ta ce, an sace mutane masu yawa bayan dubbai da suka rasa rayukansu, sakamakon tarzomar da ta mamaye duniya.

Kungiyar ta kara da cewa wasu mutanen sun fuskanci cin zarafi da fyade da kuma hare-haren kunar bakin wake. Da yake jawabi dangane da sabon rahoton na Amnesty International, janar sakatare na kungiyar a nan Jamus Selmin Caliskan ya ce mutane da dama sun hallaka sakamakon hare-haren ta'addanci da bama-bamai da kungiyar 'yan ta'addan IS da ta addabi kasashen Siriya da Iraqi da kuma kungiyar Boko Haram a Najeriya, inda ya ce kun giyoyin biyu sunma sace tare da hallaka mutane maasu tarin yawa. Caliskan ya kara da cewa rikicin kasar Ukraine tsakanin 'yan aware masu goyon bayan rasha da dakarun gwamnatin kasar ma ya lakume rayukan mutane. A hannu guda kuma kungiyar ta ce kasashen duniya 131 ana ci gaba da take hakkin dan Adam.