Amirka za ta taimaki Turai a fannin tsaro | Labarai | DW | 03.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta taimaki Turai a fannin tsaro

Shugaba Barack Obama ya ce Amirka za ta ci gaba da goyon ƙasashen Turai a cikin rikicin da ake faman yi a Yukren.

Barack Obama wanda yake yi magana a birnin Warsaw na Poland a wani mataki na farko na ziyara da yake yi a nahiyar Turai. Ya ce Amirka za ta ware kuɗaɗe kusan biliyan ɗaya, domin aike wa da ƙarin sojojin na ruwa da na sama da na ƙasa da za ta tura a gabashin Turai sannan kuma ya ƙara da cewar.

''Ina ƙoƙarin kawo ziyara a wannan ƙasar saboda amincewa da tsaron ƙasar Poland wanda ke a matsayin tsaro na haɗin gwiwa da sauran ƙasashen Turai na gabashi da na tsakiya da ke zaman garkuwa a garemu.''

Shirin wanda na ƙarfafa harkokin soji ne tare da yin attisayi soji na haɗin gwiwa tsakanin Amirka da ƙasashen Turai za a ƙaddamar da shi da zaran 'yan majalisun Amirka sun amince da shi. Shugaba Obama dai ya kira ga shugaban ƙasar Rasha Vladmir Putin da ya yi amfanin da ƙarfin faɗa a jin da yake da shi a Yukren domin su dakatar da buɗe wuta.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu