Amirka za ta taimaka wa ′yan adawa na Siriya | Labarai | DW | 27.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta taimaka wa 'yan adawa na Siriya

Shugaba Barack Obama ya buƙaci 'yan majalisun dokoki na Amirka da su amince da wani daftarin ƙudiri na samar da tallafin kuɗaɗe na biliyan 500 ga 'yan tawayen na Siriya.

Shirin zai taimaka wajen ba da horo da kuma samar da makamai ga 'yan tawayen na Siriya. Idan dai majalisun Amirka suka amince da wannan ƙudiri, to kam yin hakan zai bai wa 'yan tawayen damar yaƙar gwamnatin Bashar al Assad, da kuma kawar da duk wani yunƙurin ta'addanci da ke yin barzana ga yankin baki ɗaya.

A shekaru uku da aka yi ana gwabza yaƙi a ƙasar ta Siriya dubban jama'a suka rasa rayukansu yayin da wasu suka fice daga matsugunansu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman