1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hong Kong: Amirka za ta shiga tsakani

Ramatu Garba Baba
November 21, 2019

Majalisar Amirka ta amince da wasu dokoki da zasu hana hukumomin kasar Hong Kong mallakar makamai da ake yawan amfani dasu a kan masu zanga-zangar adawa da tsarin gwamnati na tusa keyar masu laifi zuwa Chaina.

https://p.dw.com/p/3TQnX
Hongkong - USA | Versammlung zum Menschenrechts- und Demokratiegesetz
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com/K. Tsuji

Tuni aka gabatar da kudurin a gaban Shugaba Donald Trump, inda ake jiran ya rattaba hannu. Idan har an tabbatar da dokokin biyu, za a dakatar da sayarwa gwamnatin Hong Kong din makamai musanman alburusan da take amfani dasu kan masu boren. Akwai kuma batun taka wa Chaina birki kan rawar da take takawa a rikicin kasar, batun da ake ganin ka iya shafar dangantakar kasuwanci a tsakanin Amirkan da Chainan.

Fiye da wata biyar kenan da zanga-zanga ta barke a yankin, rahotannin na nuni da cewar 'yan sanda na ci gaba da yi wa jami'ar babban birnin yankin kawanya, inda suke jiran masu zanga-zanga da suka kwashi kwanaki a ginin da su mika kansu.