Amirka za ta fara korar bakin haure | Labarai | DW | 18.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta fara korar bakin haure

Amirka za ta soma korar bakin haure daga makon gobe wadanda ke zaune a kasar ba su da takardun izinin zama.

Shugaba Donald Trump wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ya ce akwai miliyoyin mutane da ke zaune a Amirka wadanda suka shiga kasar ba cikin kai'da ba, wadanda ya ce  za su mayar da su kasashensu da gaggawa daga duk inda suka zo. Tun farko Amirka ta gargadi kasashen Amirka ta tsakiya da cewar za tai daina ba su tallafin kudade inda har ba su dau matakan dakatar da tudadar 'yan gudun hijira ba.