Amirka za ta dakatar da shirin janye dakarunta daga Afghanistan | Labarai | DW | 15.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta dakatar da shirin janye dakarunta daga Afghanistan

Dakarun Amirka kusan dubu 100 ne yanzu haka suke a kasar ta Afghanistan za su kuma ci gaba da horas da sojojin Afghanistan da kuma fatattakar mayakan Al Qaida.

Washington Obama PK Afghanistan

Shugaban Barack Obama a taron manema labaru kan kasar Afghanistan

Shugaban Amirka Barack Obama ya sanar a wannan Alhamis cewa dubun dubatan dakarun Amirka za su ci-gaba da kasancewa cikin kasar Afghanistan, sabanin yadda aka tsara da farko. Kusan dakarun Amirka dubu 100 ne yanzu haka suke a kasar ta Afghanistan, kuma karkashin tsarin da aka sabunta wadannan sojojin za su ci-gaba da zama cikin kasar a tsawon shekarar 2016. Ana sa ran rage yawansu daga tsakiyar 2016 ko farkon 2017. Wannan matakin na zama wani sauyin manufa ga Obama wanda ya so janye kusan dukkan dakarun Amirka daga Afghanistan kafin cikar wa'adin mulkinsa. Obama ya bayyana wannan matakin da cewa muhimmi ne ga muradun tsaron kasar Amirka.

"Bayan shawarwari da muka yi da tawagar tsaron kasa da kawayenmu na kasa da kasa da 'yan majalisun dokoki da kuma shugabannin Afghanistan, na ga daukar wannan matakin shi ne mafi alheri na samar da dawwamammen ci-gaba a Afghanistan. Za mu ci gaba da horas da dakarun kasar tare kuma da fatattakar kungiyar Al Qaida."