1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisar daijai na Amirka sun takawa Trump birki

Abdourahamane Hassane
March 14, 2019

'Yan majalisar datijai na Amirka sun amince da wani daftarin kudiri wanda zai tilasta wa shugaban Donald Trump janye ba da tallafin makamai ga saudiya.

https://p.dw.com/p/3F08R
Riad Donald Trump Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

Wakilai majalisar 54 suka kada kuri'a a kan kudirin yayin da 46 suka hau kujerar naki bakwai daga cikinsu kuwa 'yan jam'iyyar ta Republican. Masu aiko da rahotanni sun ce kisan dan jaridar nan na Saudiya Jamal Khasshogi da aka yi a cikin watan Oktobar shekara bara na daga cikin dalilan da suka sa 'yan majalisar datijan, suka takawa shugaba Trump birki a game da batun tallafin makamai da Amirka ke bai wa Saudiya a yakin da take yi da Yemen.