Amirka za ta bai wa Afirka Tallafi | Labarai | DW | 06.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta bai wa Afirka Tallafi

Shugaba Barack obama ya sanar da ba da tallafin sama da dala Amirka miliyan 30 ga ƙasashen Afirka don ƙarfafa kasafin kuɗaɗensu tare da saka hannayen jari na kamfanonin Amirka a nahiyar.

Obama ya ce za su saka hannun jari na tsawon lokaci da sannu a hankali a nahiyar ta Afirka ya ce ba za su iya kauda kai ba, ga sabuwar nahiyar da ke samun ci-gaba ta fannin tattalin arziki.

Haka shugaban na Amirka ya sanar da samar da biliyan 26 a wani shiri na samar da wutar lantarki a cikin ƙasashen yankin kudu da hamada. Barack Obama ya bayyana haka ne a taron Amirka da ƙasashen Afirka da ake daf da kamalawa a yau, wanda ya samu hallartar shugabannin ƙasashen Afirka kusa guda 40.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu