1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Za a bude shari'ar wanda ake zargi da kisan George Floyd

March 7, 2021

Watanni tara bayan mutuwar bakar fatar nan na Amirka George Floyd, an fara shirin gurfanar da dan sandan da ake zargin ya yi ajalinsa a gaban kuliya.

https://p.dw.com/p/3qJkB
USA Houston Beisetzung von George Floyd Joe Biden
Hoto: Reuters/D. Phillip

A ranar Litinin ake sa ran fara zabar alkalai a birnin Minneapolis da za su saurari shari'ar da za a yi wa Derek Chauvin da aka nada a hotan bidiyo ya danne wuyan bakar fata Floyd da gwiwarsa har sai da ya ce ga garinku, lamarin da ya haifar da zazzafar zanga-zanga a ciki da wajen Amirka.

Rahotanni sun ce shari'ar na bukatar samun gogaggun alkalai saboda sarkakiyarta, za a rinka watsa ta kai tsaye sannan za a samar da tsaro a harabar kotun da za a saurari karar. 

A ranar 29 ga watan na Maris ake sa ran za a fara fafata shari'ar amma sai karshen watan Afrilu ake sa ran samun kammalallen hukuncin da kotu za ta yanke a kan lamarin kisan George Floyd.