1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka tayi wa Honduras barazanar janye agaji

Zulaiha Abubakar
October 16, 2018

Rahotanni daga fadar White House sun bayyana cewar Shugaba Donald Trump yayi barazanar janye agajin kudaden da kasar Amirka take ba kasar Honduras matukar tawagar wasu 'yan ciranin kasar suka isa Amirka.

https://p.dw.com/p/36eL3
Honduras Karawane von Flüchtlingen in Richtung USA
Hoto: Reuters/J. Cabrera

A ranar Asabar din data gabata ce ayarin 'yan cirani daga Honduras suka kama hanya don isa kasar Amirka da burin gujewa kasar su da ke fama da matsanancin talauci da kuma rikici, lamarin da yanzu ya ke barazana ga karin kudin da yawansu ya kai Dala Miliyan 66 da Amirka ke shirin baiwa Hounduras a shekara ta 2019. Sai dai a nasu bangaren gungun 'yan ciranin da suka hada da yara kanana har sun kutsa kudu maso yammacin Guatemala duk kuwa da cewar jami'an tsaro sun yi nasarar chafke jagoran ayarin.