Amirka tace jiragen UAE sun kai farmaki a Libya | Labarai | DW | 26.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka tace jiragen UAE sun kai farmaki a Libya

Bayanan sirri da mahukuntan daular larabawa ba su tabbatar da sahihancinsu ba sunce jiragen nan da suka kaddamar da hare-hare a Libya a kwai na UAE a ciki.

Wasu jiragen yaki mallakar daular larabawa ta UAE sun yi ruwan bama-bamai cikin sirri kan mayakan sakai a Libya, adaidai lokacin da rikicin wannan kasa ke kara tsamari bayan da mayakan sakan Islama suka bayyana sunan Firemiyansu daga bangaren na 'yan tawaye da ke adawa.

Jamian Amirka sun tabbatar da cewa, a ranar Litinin jiragen yakin na daular larabawa ta UAE sun kai wasu hare-hare har sau biyu cikin kwanaki 7 ta hanyar amfani da wasu sansanoni a Masar.

Wani jami'i daga daular larabawan ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa babu wani abu da mahukuntan kasar sa suka fitar a dangane da rahotannin da ke fita a dangane da wannan farmaki. Shima wani jami'in Amirka da bai so a bayyana sunansa ba yace rahotannin haka suke.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu