Amirka ta yi gargadi ga Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 30.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi gargadi ga Sudan ta Kudu

Amirka ta yi barazanar sanya takunkumin karya tattalin arziki ga Sudan ta Kudu in har ba a kawo karshen rikicin da ke tsakanin gwamnati da 'yan tawayen kasar ba.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ne ya yi wannan barazanar inda ya ce in har ba su gaggauta zauna kan teburin sulhu ba to za su fuskanci takunkumi daga Amirka. Kerry dai ya bayyana hakan ne a matsayin wani mataki na kokarin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a 'yar jaririyar kasar mafi karancin shekaru a duniya. Kawo yanzu dai babu masaniya kan ko Amirkan za ta kakaba wa Sudan ta Kudun takunkumin ne a dai-dai lokacin da Kerry ke ziyara a kasar da ya bayyana cewa zai dakata a ci gaba da ziyarar aiki karon farko ta tsawon mako guda da yake yi a yanzu haka a wasu kasashen Afirka. Mahukuntan Amirkan dai na kokarin ganin sun shawo kan kasashe uku da suka fi kusanci na makwabtaka da Sudan ta Kudun da suma su sanya takunkumi kan mutanen da aka tabbatar suna da hannu a kisan fararen hula a bangarorin biyu da suke yakar juna.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman