Amirka ta yanke shawarar kai wa Siriya farmaki | Labarai | DW | 31.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yanke shawarar kai wa Siriya farmaki

Shugaban ƙasar Amirka Barack Obama ya yanke shawarar kai wa Siriya harin soji, domin ladabtar da gwamnatin Assad.

Yayinda duniya ta ke jiran jawabin shugaban ƙasar Amirka Barack Obama kan rikicin Siriya, daga ƙarshe dai shugaban ƙasar na Amirka, ya yanke shawarar cewa zai kai farmakin soja ta sama, amma babu sojan ƙasar Amirka na ƙasa da za su je cikin Siriya don yaƙi, don haka Obama ya ce farmakin taƙaitacce ne. Sai dai shugaba Obama ya ce duk da cewa yana da izinin dokar da ta ba shi ƙarfin kai harin soja, amma ya yanke shawarar kai batun gaban majalisar dokoki domin ta yanke shawarar.

A wani abin da ya shafi yaƙin Siriya, jami'an MDD da ke binciken amfani da makamai masu guba a ƙasar Siriya sun isa ƙasar Hollande bayan kammala bincike a Damaskus. Sifetocin waɗanda suka isa ƙasar a wani jirgin saman gwamnatin Jamus, za su isa cibiyar bincike ta MDD da ke birnin Hague da mota, inda za su ɗauki kwanaki suna binciken shaidar da suka samu, kan yin amfani da makamai masu guba. Jami'an binciken sun bayyana cewar binciken na su yana buƙatar lokaci.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdourrahmane Hassane