Amirka ta yaba da tsarin demokradiyyar Senegal | Siyasa | DW | 27.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amirka ta yaba da tsarin demokradiyyar Senegal

Shugaba Obama ya bukaci Senegal ta mutunta masu auren jinsi domin karfafa demokradiyyarta.

Shugaban Amirka, wanda ya fara rangadinsa na wasu kasashen Afirka da yada zango a Senegal, ya yaba da irin gindin zaman da tsarin demokaradiyya ya samu a kasar, wadda ta ciri tuta a fagen rashin samun juyin mulkin soji tunda ta samu 'yancinta daga Turawan mulkin mallaka.

Ya ce Senegal na sahun farko a jerin kasashen da Amirka ke kawance dasu a yankin. Yana mai bayyana farin cikinsa game da sauye-sauyen da kasar ke samar wa domin tabbatar da cibiyoyin da ke zama sinadaran tsarin na demokradiyya. A bisa wannan dalilin ne shugaban na Amirka - ta bakin tafinta -ya ce Senegal ta zama abar misali a nahiyar:

Ya ce "Senegal kasa ce da mulkin demokradiyya ke da inganci a nahiyar Afirka. Tana kuma zama tamkar abar misali wajen kyautata rayuwar 'yan kasa. Kasar tana bisa tafarki na gari. Kasa ce kuma da ya kamata ta zama abar koyi ga sauran kasashen Afirka."

Senegal's newly inaugurated President Macky Sall waves to supporters as he travels to the presidential palace to take up residence, in Dakar, Senegal Monday, April 2, 2012. Sall took the oath of office Monday in a ceremony held one week after the country's longtime incumbent conceded defeat only hours after polls closed. The presidential runoff vote solidified the country's reputation as one of the few mature democracies in western Africa, where the unpopular president was ousted at the ballot box instead of a coup. (Foto:Rebecca Blackwell/AP/dapd)

Shugaba Macky Sall

Mutunta masu auren jinsi a Senegal

Duk da yabon da Senegal ta samu dangane da ingantaccen tsarin demokradiyya dai, shugaban na Amirka ya bukaci ta bullo da muhimman matakai da kuma dokokin da za su tabbatar da bada kariya ga abin da ya ce 'yancin da 'yan kasa ke da shi wajen neman biyan bukatunsu na sha'awa. Ya ce kamata yayi hukumomin su kare 'yancin auren jinsi guda ta hanyar bullo da dokoki, inda ya ce hukuncin da kotun kolin Amirka ta zartar a baya-bayan nan dangane da batun auren jinsi guda, wata nasara ce ga tafarkin demokradiyya a kasar ta Amirka, wadda kuma ya ce lokaci yayi da ya kamata wannan nasarar ta tsallaka zuwa sauran kasashen duniya musamman ma nahiyar Afirka.

Da yake mayar da matani dangane da kalaman na Obama kuwa, shugaban Senegal Macky Sall watsi yayi da bukatar, yana mai jaddada cewar hakan kuma ba ya nufin rashin mutunta 'yancin masu auren jinsi guda bane:

"Manufofin da ya kamata a yi aiki dasu, su ne mutunta dan adam da kuma kawar da wariya a tsakanin al'umma. Wannan abu ne da zamani ya kawo, wanda kuma ya kamata kasashe su runguma. Abin da ya shafi Senegal, kasa ce mai tausayawa, wacce kuma ba ruwanta da abin da ya shafi nuna wariya dangane da abin da ya shafi 'yancin dan Adam. Ba a shirye muke ba mu amince da auren jinsi."

Matsayin 'yan Afirka dangane da auren jinsi

Dama dai wani binciken da cibiyar Pew ta gudanar a ranar hudu ga watan Yunin nan a kasashen da suka hada da Senegal da Kenya da Ghana da Uganda da kuma Najeriya ya gano cewar mutane 9 cikin 10 sun yi amannar cewar bai kamata al'umma ta yarda da masu auren jinsi guda ba.

A dai lokacin ziyarar, shugaba Obama, tare da rakiyar mai dakinsa Michell da kuma 'ya'yansu biyu dai, sun ziyarci tsibirin Goree da ke zama zangon safarar bayi daga Afirka a lokacin mulkin mallaka, lamarin da ya kwatanta da cewar manuniya ce ga rashin kare mutuncin dan Adam a wancan lokacin, wanda kuma ya ce darasi ne a gareshi na ya tashi tsaye domin kare hakkin kowane dan Adam.

Kazalika shugaba Obama ya gana da shugabannin kungiyoyin fararen hula da kuma ziyartar kotun kolin Senegal domin nuna muhimmancin sashen shari'a da mutunta doka ga ci gaban nahiyar Afirka.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin