SiyasaGabas ta Tsakiya
Chaina ta zargi Amirka da cutar mata da 'yan sama jannati
December 28, 2021Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta sanar a wannan Talata cewa Amirka ta yi watsi da ka'idojin sararin samaniya, lamarin da ya jefa mata 'yan sama jannati cikin hatsari. Hukumomin Chaina sun shaidawa MDD cewa saura kiris tawagar 'yan sama jannatinta ta yi karo da ta wani kamfani na Amirka.
Kamfanin da Chainan ke zargi da kawo wa tasharta ta 'yan sama jannatin cikas mallakin 'yan kasuwa ne a Amirka. Sai dai hukumomin Beijing sun ce a bisa dokar sararin samaniya kasashe ne ke daukar alhakin abin da kamfanoni suka aikata.