1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta sanya takunkumi kan 'yan Kwango

September 29, 2016

Wasu na hannu daman shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar dimukradiyyar Kwango sun shiga sahun manyan jami'an kasar da Amirka ke zargi da cin mutuncin 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/2QkQP
Kongo Präsident Joseph Kabila
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Bompengo

Hukumomin kasar Amirka sun sanya takunkumi kan wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Kwango biyu bisa zargin yin amfani da hanyoyin da b su dace ba wajen cin zarafin 'yan adawan kasar. Ana dai ganin cewar akwai kusanci mai karfi tsakanin mutanen biyu Gabriel Amisi Kumba da John Numbi da shugaban kasar shugaba Joseph kabila. To sai dai kawo yanzu mutanen biyu da ake zargin ba su kai ga yin martani kan wannan mataki ba.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta HRW ta ce daya daga cikin jami'an da aka kakabawa takunkumin Amisi Gabriel Amisi, na cikin wadanda jami'an sojin kasar ta Kwango suka wankeshi daga tuhumar cin zarafin al'umma shekaru iyu da suka gabata. Kasar Amirka dai na cikin kasashen da ake ci gaba da nuna damuwa game da matsin lamba ga Jamhuriyar Kwango kan yadda tarzoma zabe ya dabaibaye kasar wanda ya kai ga dage babban zaben kasar zuwa shekara mai zuwa.