Amirka ta samu sabon sakataren harkokin waje
December 22, 2012A cikin jawabin da ya yi a birnin Washington, Obama ya ce Kerry ya cancanci rike wannan mukami. Kerry mai shekaru 69 da ke shugabantar komitin harkokin waje a majlisar dattawa zai gaji Hillary Clinton da ke shirin sauka daga wannan mukami da ta ce ba za ta nemi yin wa'adi na biyu ba. Da farko an so ne a ba da wannan mukami ga Susan Rice da ke wakiltar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya. To amma sai 'yan Republikan suka ce su ba za su kada kuri'ar aimicewa da ba ta wannan mukami ba. Shi dai Kerry kwararren masani ne a kan harkokin waje wanda kuma a lokuta da dama ya wakilci Obama a lokutan rikice rikice. 'Yan Republikan suna kuma mutunta shi yadda ya kamata. Kerry shi ne ya tsaya da tutar jam'iyyar Democrat a zaben shugaban kasa a shekarar 2004 , to amma sai ya sha kayi a hannun George W Bush.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal