1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan fursunan Guantanamo ya koma gida

Abdul-raheem Hassan
July 20, 2021

Abdullatif Nasser mai shekaru 56, ya koma cikin danginsa bayan amsa tambayoyin 'yan sandan Moroko, shi ne na farko da gwamnatin Joe Biden ta maida shi karkashin kulawar hukumomin kasarsa ta haihuwa daga Guantanamo.

https://p.dw.com/p/3xl3C
Kuba Guantanamo | Camp Delta
Hoto: US Navy/Spc.Cody Black//REUTERS

A karon farko bayan shekaru 19 hukumomin Amirka sun sako wani ba Amirke dan asalin Moroko da aka tsare a Guantanamo ba tare da tuhuma ba kan zargin ta'addanci.

Yanzu haka dai kusan mutane 800 ne suka dandana zaman kurkukun Guatanamo Bay. Akwai mutane 39 da ke tsare hayar yanzu 10 daga ciki sun cancanji sauya musu sheka, zuwa asalin kasashensu kamar Yemen da Pakistan da Tunisiya da Aljeriya da kuma hadaddiyar daular Larabawa Dubai.