1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta lalata makaman 'yan Houthi a tekun Bahar Maliya

February 9, 2024

Rundunar sojin Amirka ta ce ta kai sabbin hare-hare kan makaman 'yan tawayen Houthi na Yemen, wadanda suka shirya kai hare-hare da su a tekun Bahar Maliya.

https://p.dw.com/p/4cD0d
Amirka ta lalata makaman 'yan Houthi a tekun Bahar Maliya
Amirka ta lalata makaman 'yan Houthi a tekun Bahar MaliyaHoto: US NAVY/AFP

A sakon da ta wallafa a shafinta na X da aka fi sani da Twitter a baya, rundunar ta ce ta kai harin ne kan wasu jiragen ruwa marasa matuka guda hudu da wasu jiragen makamai masu linzami guda 7 a tekun, makaman da ke zama babbar barazana ga sojojin ruwan Amirka da sauran jiragen ruwan 'yan kasuwa.

Karin bayani: Amurka da Burtaniya sun kai sabbin hare-hare Yemen

Rundunar ta kara da cewa, matakin da ta dauka zai kara tabbatar da tsaron ruwan kasa da kasa da ma karin kariya ga jiragen ruwan. A baya-bayan nan 'yan tawayen Houthi na kai hare-hare kan jiragen ruwa, lamarin da ya haifar wa kamfanoni da dama kaurace wa tekun.