SiyasaJamus
Amirka ta jajanta rikicin yankin Tigray
March 18, 2021Talla
Shugaba Biden zai tura da Sanata Chris Coons da ke zama na hannun damansa kasar, kana kuma ya tuntubi kungiyar Tarayyar Afirka. Ana kuma sa ran Coons zai bar Amirka zuwa Habasha a wannan rana ta Alhamis.
Duk da yake gwamnati ta ce an daina yaki a yanki amma ta yi amannar cewa ana kai hare-hare ta bayan fage. Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu yayin da dubban daruruwa suka rasa matsugunansu wasu kuma ke bukatar abinci da ruwa da kuma magunguna a yankin da ke da yawan al'umma kimanin miliyan biyar.