1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta mara baya ga masu fafutuka a Hong Kong

Suleiman Babayo AS
November 28, 2019

Shugaba Donald Trump na Amirka ya saka hannu kan dokar goyon bayan masu zanga-zanga na Hong Kong abin da ya fusata mahukuntan Chaina.

https://p.dw.com/p/3TrYh
HongKong Protest
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. Yu

Shugaba Donald Trump na Amirka ya saka hannu kan ayar dokar da majilsar dokoki ta amince da ita kan goyon bayan masu zanga-zanga a yankin Hong-Kong na Chaina, abin da zai janyo saka takunkumi ga duk wadanda aka samu da cin zarafin dan Adam. Shugaba Trump ya ce ya amince da dokar domin nuna mutunta Shugaba Xi Jinping na Chaina.

Tuni masu zanga-zanga na Hong Kong suka yi maraba da wannan ayar dokar yayin da mahukuntan Chaina suka soki lamarin tare da bazanar mayar da martani. Saka hannu kan ayar dokar na zuwa ne yayin da Amirka ke neman ganin an kulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da Chaina gabanin zaben da za a yi a kasar ta Amirka a shekara mai zuwa ta 2020.