1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An kwashe fiye da mutane 70,000 daga Afghanistan

Suleiman Babayo ZMA
August 25, 2021

Yayin taron kungiyar G7 manyan kawayen Amirka sun gaza shawo kan shugaban kasar ta Amirka Joe Biden bisa matakin tsawaita lokacin janye dakarun kasashen daga Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3zSPq
USA I Joe Biden über die Situation in Afghanistan
Hoto: Jim Watson/AFP

Amirka ta shiga takun saka da wasu kawayenta bisa matakin Shugaban kasar Joe Biden wanda ya tsaya kai da fata cewa za a kammala janye dakarun kasar daga Afghanistan zuwa ranar 31 ga wannan wata na Agusta, duk halin da ake ciki kan kwashe mutane daga kasar sakamakon kwace madafun iko da mayakan Taliban suka yi.

Yayin taron gaggan kasashe masu arzikin masana'antu na duniya na G7 ta hanyar bidiyo da ya wakana a wannan Talata da ta gabata Biden ya ce babu ja-da baya kan matakin kammala janye dakarun kasarsa duk bukatar tsawaita lokacin daga kasashe masu dasawa da Amirka.

Tuni mayakan kungiyar Taliban da suke rike da galibin sassan Afghansitan suka ce babu yuwuwar amince da tsawaita lokacin na ficewar dakarun kasashen duniya daga cikin kasar.

Kawo yanzu fiye da mutane 70,000 aka kwashe daga filin jirgin saman birnin Kabul na Aghansitan, yayin da dubban suke ci gaba da jiran tsammanin a kwashe su.