1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta bukaci Iran ta bada hadin kai ga AEIA

March 6, 2013

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da kasar Amirka ke kira da kasar Iran ta bayana matsayin shirinta na nukiliya ga hukumar kasa da kasa ta AEIA.

https://p.dw.com/p/17s95
Hoto: aeoi.org.ir

Kasar Amirka ta bukaci da hukumomin kasar Iran da su bada hadin kai ga hukumar makamashi ta kasa da ksa domin binciken wasu tashoshinta na nukiliya . Wakilin Amurka a hukumar makamashin ta AIEA Joseph Macmanus,yace duniya fa ta gaji da kallon kasar Iran na daukar kai ga maganar nukiliyarta, don haka lokaci yayi inda ya kamata a yita a kare da kasar don kowa ya kama gabansa.
Bayan shekaru kusan goma ana taci bata ci ba da kasar ta Iran a dangane da shirinta na nukiliya, kawo yanzu dai hukumar ta makamashi ta kasa da kasa bata tantance manufar kasar ta Iran ba a dangane da batun, shirin da hukumomin na Iran suka jajirce cewar na samar da makamashi ne domin aikin farar hulla hujjar da kasashen duniya suka yi watsi da ita suna zargin kasar da shirya makaman kare dangi.
Kawo yanzu dai Iran din bata maida martani ba a kan bukatar ta Amirka da ma hukumar ta AIEA.

Mwallafi: Issoufou Mamane
Edita: Saleh Umar Saleh