1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Amirka ta ce kisan kare dangi aka yi wa Armeniyawa

Binta Aliyu Zurmi SB
April 24, 2021

Fiye da shekaru 100 bayan yakin duniya na daya, yanzu Amirka ta amince da cewa abin da ya faru da Armeniyawa kisan kare dangi ne karkashin Daular Ottoman.

https://p.dw.com/p/3sWo4
Armenien Gedenken Massaker an den Armeniern während des Ersten Weltkriegs
Hoto: Ashot Gazazyan/DW

A karon farko, bayan kwashe samam da shekaru dari da kissan da aka yi wa daruruwan alummar kasar Armenia, Amirka ta ayyana al'amarin a matsayin kisan kiyashi.


Shugaba Joe Biden shi ne shugaban Amirka na farko da ya yi amfani da kalmar kisan kare dangi a kan kisan da ya faru a zamanin tsohuwar Daular Ottoman da ya faru daga karni na 14 zuwa na 20.

da yake jawabi a yau domin tunawa da ranar, shugaba Biden ya ce sun ayyana lamarin a matsayin na kisan kiyashi ba wai don sun son mayar da hannun agogo baya ba face don ganin hakan bai sake faruwa ba nan gaba. Kasashen duniya irinsu Faransa da Jamus da Kanada da ma Rasha sun jima da ayyana wannan abu a matsayin na kare dangi lamarin da ake jinjinawa Shugaba Joe Biden na Amirka kan bin sahun sauran kasashe.

Tuni shugaban Turkiyya ya mayar da martanin cewa masana tarihi suke da alhakin fadin abin da ya faru ba wai 'yan siyasa ba. Firaministan Armeniya ya jinjinawa Biden da wannan mataki.