1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Shekaru 100 da kisan kiyashi a Oklahoma

June 2, 2021

Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya yi ikrarin cewa har kawo yanzu akwai sauran burbushin rikice-rikicen wariyar launin fata.

https://p.dw.com/p/3uKDT
USA Präsident Biden 100. Jahrestag Massaker von Tulsa
Hoto: Carlos Barria/REUTERS

Shugaban ya baiyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ga yankin Tulsa na jihar Oklahoma a jiya Talata, inda aka yi wa daruruwan Amirkawa bakaken fata kisan kare dangi a shekarar 1921.

Manufar ziyarar ta sa dai ita ce nuna alhininsa ga rikicin nuna wariya mafi muni da ya auku a gundumar greenwood na jihar a wancan lokacin, kana ziyarar Biden din na zuwa ne yayin da kasar ke fuskantar tarin mutane da ke zanga-zangar nuna adawa da cin zarafin 'yan sanda ke yi musu da nuna wariyar launin fata ga bakake. 

A ranakun 31 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni na shekarar 1921, rikicin kabilanci ya barke a yankin dake cikin yankunan da suka fi yawan bakaken fata a kasar, inda aka hallaka kimanin bakaken fata 300 tare da kone gidaje. Tuni dai fadar White House ta sanar da jerin manufofinta na magance matsalar nuna wariya, ciki har da saka hannun jarin biliyoyin daloli ga ire-iren wadannan yankuna dake fama da radadin talauci.